logo

HAUSA

Yadda Bikin CIIE Ya Inganta Ci Gaban Sin Da Sassan Kasa Da Kasa

2023-11-06 13:41:44 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kamfanin Johnson and Johson na Amurka, kuma jagoran kamfanin a kasar Sin Song Weiqun, ya ce ya ji yadda Sin ke nacewa bude kofa ga waje, da kuma sauke nauyin da ke wuyanta na inganta cigaban tattalin arzikin duniya, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Song ya bayyana hakan ne bayan nazartar wasikar taya murna da shugaban Sin Xi Jinping ta gabatar ga bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na shida, inda ya kara da cewa, wasikar ta karfafa gwiwar kamfanin Johnson and Johson wajen ci gaba da neman samun bunkasuwa a kasar Sin.

Shekarar bana ita ce ta cika shekaru 45 da Sin ta gabatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare a gida, kuma ta cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”. A wannan shekara mai ma’anar musamman ne kuma ake gudanar da bikin CIIE karo na shida.

Yadda kamfanonin kasa da kasa masu dimbin yawa suka shiga bikin CIIE na bana bisa shirin da aka tsara, ya shaida kokarin kasar Sin na cika alkawarinta da kara bude kofarta ga kasashen waje. A yayin bikin CIIE na wannan karo, bangaren Sin ya fitar da jerin manufofi, wadanda suka hada da habaka shigo da kayayyaki daga ketare, da kafa yankin gwajin cinikayya maras shige ko FTZ da sauransu, lamarin da zai taimaka wa kamfanonin kasa da kasa wajen kara samun cigaba a Sin, kana zai shaida yadda bikin CIIE ke bayar da gudummawa wajen inganta matakin bude kofa mai babban matsayi. 

Bikin CIIE dandamali ne na cudanyar sassa daban daban na duniya. Kuma a nan gaba, bikin zai kara samar da hidimomi masu inganci da zai amfani kasa da kasa, lamarin da ke nuna cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka kan ra’ayin kasancewar bangarori daban daban, da nuna adawa da ra’ayoyin rufe kasa, da neman raba-gari da sauran kasashe. Cikin sahihanci, Sin za ta taimakawa sassan kasa da kasa wajen samun cigaba, tare da raya tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa ga juna. 

Ko shakka babu baje kolin CIIE ya kawo kwarin gwiwa da karfi ga duniya, a wannan yanayin da ake ciki na barkewar rikice-rikice tsakanin bangarori daban daban, da daukar matakai a makare, da kuma tabarbarewar tattalin arzikin duniya. (Safiyah Ma)