Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kewaye birnin Gaza yayin da adadin Falasdinawa da suka rasu ya kai 9,770
2023-11-06 10:11:41 CMG Hausa
Rundunar sojojin Isra’ila ta ce dakarunta sun kai kan iyakar ruwa ta birnin Gaza, sun kuma yiwa mayakan Hamas dake cikin birnin kawanya, a gabar da adadin Falasdinawa da suka rasu, sakamakon hare-haren sojojin Isra’ilan ya kai mutum 9,770.
Rundunar dakarun na Isra’ila ta ce sojojinta sun kewaye Gaza ne da nufin kaddamar da hare-hare kan wasu zababbun wurare, ciki har da kadarori masu muhimmanci, da cibiyoyin ba da umarni na mayakan Hamas.
A wani ci gaban kuma, mahukunta a Iran sun ce jagoran kungiyar Hamas Ismail Haniyeh, ya gana da shugaban addini na kasar Ali Khamenei a jiya Lahadi a birnin Tehran. Yayin ganawar tasu, Khamenei ya jaddada tabbatacciyar manufar Iran ta goyon bayan tirjiyar da Falasdinawa ke yi ga dakarun Isra’ila.
A daya bangaren kuma, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry, ya ce tarnakin da tsagin Isra’ila ke yi ga shirin shigar da kayayyaki, da ci gaba da lugudan wuta kan mashigar Rafah da sojojin Isra’ilan ke yi, sun haifar da jinkirin shigar da kayan agajin jin kai sassan zirin Gaza, kuma hakan ya dorawa Masar karin nauyi.
Wata majiyar tsaro da ta bukaci a boye sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa a jiya Lahadi, kasar Masar ta aike da manyan motoci 75 makare da abinci, da ruwa, da kayan jinya ta mashigar Rafah zuwa Gaza, kuma da wannan karin kayan tallafi, jimillar manyan motocin dakon kaya da suka shiga Gaza, tun daga ranar 21 ga watan Oktoba da ya shude kawo yanzu, sun kai kusa 500. (Saminu Alhassan)