logo

HAUSA

Blinken ya ki amincewa da bukatar Abbas na tsagaita wuta a Gaza

2023-11-06 16:01:37 CMG Hausa

 

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi watsi da bukatar shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas na tsagaita bude wuta a zirin Gaza, a cewar wani jami’in Falasdinu.

Jami’in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Blinken ya jaddada a yayin ganawarsa da Abbas a birnin Ramallah dake gabar yammacin kogin Jordan “hakkin Isra’ila na kare kanta da ci gaba da yakin da take yi” a Gaza.

Ziyarar Blinken a Ramallah ya dauki kimanin sa’a guda, inda ya gana da Abbas da manyan mukarrabansa inda suka tattauna rikicin Isra’ila da Hamas.

Ya ce Blinken ya yi alkawarin matsawa Isra’ila lamba don kauce wa cutar da fararen hula da samar da amintattun hanyoyin kai agajin jin kai, amma ya ki tattauna hanyoyin tsagaita bude wuta a wannan mataki. (Yahaya)