logo

HAUSA

Bikin CIIE ya sa kayayyakin kasashen Afirka samun karbuwa

2023-11-06 16:50:15 CMG Hausa

A jiya Lahadi, an bude bikin baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na 6 a birnin Shanghai na kasar Sin.

Bisa matsayinsa na wani muhimmin bikin da ake tallata kayayyaki, da kulla huldar ciniki, bikin CIIE na ta samun karbuwa tsakanin ‘yan kasuwar kasashen Afirka. A wajen biki na wannan karo, an kawo hulunan ciyayi kirar kasar Togo, da waken koko na kasar Zimbabwe, da ridi na kasar Mali, da kashu din kasar Guinea-Bissau, da abarbar kasar Benin, da duwatsu masu kunshe da ma’adinai na kasar Afirka ta Kudu, da dai sauransu. Wasu kamfanoni 6 na kasar Najeriya ma suna cikin mahalarta bikin baje kolin, inda suka nuna wasu lu’u-lu’u, da amfanin gona na musamman na Najeriya.

Sai dai daya daga cikin kayayyakin da suka fi samun karbuwa wajen bikin CIIE na wannan karo, shi ne wani nau’in abarba da ake kiranta “Burodi mai zaki” ta kasar Benin. Cikin abarbar yana da launin fari, kana yana kunshe da dimbin ruwa mai zaki. Duk wanda ya sha abarbar sai ya yabe ta.

Bisa bikin CIIE na wannan karo, Sinawa sun fara sanin wannan nau’in abarba a karon farko. A nasa bangare, Simon Adovelande, jakadan kasar Benin a kasar Sin, ya nuna kyakkyawan fata game da ci gaban kasarsa ta bangaren samar da abarba, ganin yadda wannan nau’in ’ya’yan itatuwa ke samun karbuwa sosai a kasar Sin. Ko da yake kasar Benin ta kan samar da abarba kimanin ton dubu 400 a duk shekara, wadanda ta fi fitarwa zuwa kasashen Turai da na Afirka, amma Adovelande yana sa ran ganin yawan abarbar da kasar Benin ke fitarwa zuwa kasar Sin kacal ta kai ton dubu 300 a duk shekara, nan ba da dadewa ba.

Cikin kayayyakin kasashen Afirka da aka nuna a wajen bikin CIIE, ban da abarbar kasar Benin da ta fara samun karbuwa, akwai ’ya’yan itatuwa na Avacado din kasar Kenya, wanda tun tuni ya yi farin jini. A shekarar 2018, an nuna daskararren Avacado na kasar Kenya a bikin CIIE a karon farko. Sa’an nan, kasashen Sin da Kenya sun kulla wata yarjejeniya a shekarar 2022, don tabbatar da fitar da Avacado din kasar Kenya zuwa kasar Sin. Daga bisani, Avacado din kasar Kenya ya shiga kasuwannin kasar Sin, da fara zama kayan marmari mai samun karbuwa sosai. Zuwa yanzu, kashi 30% na Avacado din kasar Kenya, an fitar da su zuwa kasar Sin. Kana ana sa ran ganin karuwar jimillar a nan gaba. Ban da haka, hukumomi masu kula da aikin gona na kasar Kenya sun kiyasta cewa, manoman Avacado na kasar Kenya sun samu karuwar kudin shiga da ta kai kashi 30% zuwa 50%, ta hanyar fitar da Avacado zuwa kasar Sin.

Bikin CIIE shi ne na farko a duniya da ya mai da hankali a kan baje kolin kayayyakin da ake shigarwa da su, wanda a kan kaddamar da shi a farkon watan Nuwamban kowace shekara. A bana, an samu manyan baki mahalarta taron da suka zo daga kasashe da yankuna, da kungiyoyin kasa da kasa, har 154. Kana a shekarar 2022, kasar Sin ta shigo da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amukra tiriliyan 2.7, adadin da ya kusan kai kashi 11% na dukkan kayayyakin da ake shigarwa kasuwannin duniya.

Haka zalika, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, darajar hidimomin da kasar Sin ke shigowa da su ta karu da kashi 22.4%, bisa makamancin lokacin bara. Hakika yadda kasar Sin ke neman shigowa da karin kayayyaki daga ketare, zai iya sa kaimi ga aikin samar da kayayyaki, da bangaren samar da guraben aikin yi, da baiwa jama’a karin kudin shiga, a sauran kasashe, gami da daidaita tsarin da ake bi wajen raba kayayyakin da ake bukata don raya masana’antu. Hakan ya yi kama da maganar Christine Lagarde, tsohuwar babbar darektar asusun ba da lamuni na duniya IMF, wadda a yayin bikin CIIE karon farko da ya gudana a shekarar 2018, ta fada, cewa bikin ya nuna yadda kasar Sin take kokarin sauya fasalin aikin ciniki na duniya, wanda zai amfani kasar Sin, gami da daukacin duniya baki daya.

Ban da haka, yadda kayayyakin kasashen Afirka suka fara samun karbuwa a kasuwannin duniya ta bikin CIIE, ya nuna ma’anar bikin da kasar Sin take gudanarwa ga kasashe masu tasowa. A cewar Stephen Kargbo, wakilin kungiyar raya masana’antu ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sin, dimbin kamfanoni na kasarsa, wato Saliyo, da na sauran kasashe daban daban dake nahiyar Afirka, sun halarci bikin CIIE na bana, inda suka samu damar nuna fasahohi, da kayayyakinsu a wannan muhimmin dandali na kasa da kasa. Ya ce, “Bikin CIIE na kasar Sin ya ba mabambantan kasashe damar more ci gaban tattalin arzikin duniya, kana kasar ba za ta taba barin wani a baya ba.” (Bello Wang)