Sakatare janar na MDD ya kadu da harin Isra’ila a Gaza kan jerin gwanon motocin daukar mara lafiya
2023-11-04 20:09:23 CMG Hausa
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ya kadu da jin labarin harin da aka kai kan jerin gwanon motocin daukar mara lafiya a wajen asibitin Al Shifa a Gaza, inda ya sabunta kiransa na dakatar da bude wuta domin jin kai.
Antonio Guterres ya ce, wajibi ne a girmama dokar kasa da kasa. Kuma dole ne a kare fararen hula da kayayyakinsu, ciki har da ma’aikatan jin kai da na jinya da kadarorinsu. Haka kuma bai dace a yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa ba.
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta tabbatar da cewa, an kai harin kan motar daukar mara lafiya, amma Hamas ce ke amfani da ita, tana mai zargin kungiyar da jigilar mayakanta da makamai a ciki.
Har ila yau, dakarun Isra’ila sun ce, an kashe mayakan Hamas dake cikin motar, amma ba tare da bayyana adadinsu ba.
Sai dai ma’aikatar lafiya ta Gaza dake karkashin Hamas, ta ce Isra’ila ta kai harin kan motocin daukar mara lafiya, wadanda ke kwashe mutanen da suka jikkata daga arewacin Gaza da aka yi wa kawanya, inda mutane 15 suka mutu yayin da 60 suka jikkata. (Fa’iza Mustapha)