CIIE: ‘Yan Kasuwan Kasa Da Kasa Na Alla-alla Wajen Yin Amfani Da Damar Ci Gaban Kasar Sin
2023-11-03 20:45:33 CMG Hausa
Za a gudanar da taron baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na 6 daga ranar 5 zuwa 10 ga wata a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin. A yau Jumma’a ne aka kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da taron. Baki daga kasashe, yankuna da hukumomin kasa da kasa guda 154 da kamfanoni fiye da 3400 na duniya za su halarci taron cikin kwanaki da dama masu zuwa, ciki had da kamfanoni masu alaka da raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” sama da 1500. Abin da kamata a lura da shi, shi ne a cikin wadannan kamfanoni fiye da 3400, wasu da dama sun halarci taron na CIIE sau 6 baki daya.
Mene ne dalilin hakan? Saboda halartar taron na CIIE ya ba su damar samun bunkasuwa. Kayayyakin da suke baje koli a taron CIIE sun zama hajojin da suke sayarwa a kasar Sin, kana suna zuba jari a kasar Sin a maimakon halartar taron na CIIE kawai. Tun tuni kasar Sin ta yi alkawarin mayar da kasuwar Sin zuwa kasuwar duniya mai kunshe da kowa. Ta kuma cika alkawarinta a zahiri. Ta yi ta ba kamfanonin kasa da kasa damarmakin samun ci gaba.
Alkaluman tattalin arzikin kasar Sin na watanni 9 na farkon bana kuma sun tabbatar da haka. Karuwar tattalin arzikin kasar Sin wato GDP ta kai kaso 5.2 a watanni 9 na farkon bana bisa makamancin lokaci na shekarar bara, karuwar ta fi ta rukunonin duniya masu karfin tattalin arziki. Ciki kuma karuwar yin sayayya ta fi jan hankali, wadda ta taimakawa karuwar GDP har kaso 4.4. Wadannan alkaluma sun samar da kamfanoni masu jarin waje kyawawan damarmaki.
Baya ga dimbin al’umma mai yawan biliyan 1.4 da kuma masu matsakaitan kudin shiga sama da miliyan 400, gwamnatin kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan bude kofa ga kasashen ketare, lamarin da ya jawo hankalin kamfanoni masu jarin waje da dama, musamman ma shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da kasar Sin ke kokarin aiwatarwa cikin hadin gwiwar kasa da kasa, tana amfanawa kasashen duniya sosai. A sashen nune-nunen kasa da kasa a taron CIIE na wannan karo, akwai kasashe 64 da suke raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” daga cikin dukkan kasashen 72. A ‘yan kwanakin baya, jiragen kasa da ke tafiya tsakanin kasar Sin da kasashen Turai suna ta jigilar kayayyakin kasashen da ke raya shawarar zuwa taron CIIE.
Har ila yau taron na CIIE na bai wa daukacin kasashen duniya damar samun ci gaba, musamman ma taimakawa kasashe masu rauni samun bunkasuwa, lamarin da ya burge wasu kamfanoni. Kasashe mafiya karancin ci gaba, wadanda suke raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” sun samu wurin nune-nune ba tare da biyan kudi ba a taron na CIIE, tare da samun kudin tallafin yin nune-nune da haraji mai gatanci kan kayayyakin da za su nuna, ta yadda kayayyakinsu masu halin musamman za su samu damar shiga kasuwar kasar Sin
Kokarin da kasar Sin take bayarwa ya shaida cewa, manufar kasar Sin ta shirya taron na CIIE ita ce kara azama kan gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkan bil Adama. Taron na CIIE ya sanya kasashen duniya sun kara sanin aniyar kasar Sin ta bin manufar cudanyar sassa daban daban da samar wa kasashen duniya damar ci gaba, da kuma matakan da take dauka. Da ma wasu daga kasashen yamma sun yi shelar cewa, masu jarin waje sun janye jiki daga kasar Sin, amma yadda kamfanoni masu jarin waje suke halartar taron CIIE sau da dama, ya sanya gaskiya za ta yi halin ta.
Hukumar kara azama kan cinikayya ta kasar Sin ta kaddamar da rahoto a kwanan baya cewa, kamfanoni masu jarin waje da aka yi musu tambaya wadanda yawansu ya wuce kaso 80, sun gamsu da yanayin kasuwancin kasar Sin. Ya zuwa yanzu kasuwar kasar Sin na jan hankalinsu sosai. Bude taron na CIIE karo na 6 za ta kara nuna yadda ake yin amfani da damar da kasar Sin ke samarwa. (Tasallah Yuan)