logo

HAUSA

Sin da Amurka za su tattauna kan sauyin yanayi kafin COP28

2023-11-03 11:02:55 CMG Hausa

Ma’aikatar muhalli ta kasar Sin ta bayyana a jiya Alhamis cewa, wakilin musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua, zai gana da takwaransa na Amurka John Kerry a jihar Califonia daga ranar 4 zuwa 7 ga watan Nuwamba.

Bangarorin biyu za su yi musayar ra’ayi kan yadda za a ciyar da harkokin yanayi gaba da hadin gwiwa, da kuma sa kaimi ga samun nasarar taron sauyin yanayi na MDD a Dubai, a cewar wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar.

An shirya gudanar da taro karo na 28 na majalisar zartaswa ko COP a takaice, na MDD kan sauyin yanayi a Dubai na Hadaddiyar Daulolin Larabawa daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba. (Muhammed Yahaya)