logo

HAUSA

Jakadan Palasdinu a Najeriya ya ziyarci jihar Kano

2023-11-03 10:16:36 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Kano dake arewacin Najeriya ta bayyana goyon bayanta ga zaman lafiyar duniya baki daya, tare da yabawa kasashen da suke fadi tashin tabbatar da ganin an kawo karshen rikicin Palasdinu da kasar Isra’ila.

Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan jiya Alhamis, 2 ga wata lokacin da jakadan Palasdinu a Najeriya Abdallah Abu Shawish ya ziyarce shi a gidan gwamnatin jihar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Gwamnan jihar ta Kano wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Dr Baffa Bichi ya ce, yankin gabas ta tsakiya yanki ne da yake da matukar muhimmanci ga al’ummar musulmin duniya, kuma yanki ne da yake taka rawa a siyasar tattalin arzikin duniya, a don haka zaman lafiyarsa babbar fa’ida ce ga kowa.

Inda ya ce, ya dace Isra’ila da sauran kasashen da suke mara mata baya su sake tunani a kan luguden bama-bamai da yanzu haka ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da suka hada da mata da kananan yara, baya ga lalata kaddarori.

A jawabinsa jakadan na kasar Palasdinu a Najeriya Mr Abdallah Abu Shawish ya ce, Isra’ila tana neman ta karfin tuwo ta kori Palasdinawa daga yankin da Burtaniya ta mallaka musu tun a shekarar 1917, lamarin da ya bayyana da cewa zalinci ne matuka.

“Wannan yaki ko kadan ba za a ce yaki ne tsakanin Hamas da dakarun Isra’ila ba, yaki ne kawai tsakanin Isra’ila da al’ummar Palasdinu wanda kuma suka hada da Musulmai da Kiristoci, daman dai akwai ajandar da Isra’ila take son cimmmawa na korar Palasdinawa daga yankin zirin Gaza, kuma ta tsara wannan shiri ne tun a shekarar 1994. A saboda haka mu Palasdinawa muna tabbatarwa duniya cewa za mu tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ganin babu wanda zai fitar da mu daga kasarmu.” (Garba Abdullahi Bagwai)