Hadarin da ya auku ya bankado karyar Japan game da ruwan dagwalon nukiliyar da take zubarwa a teku
2023-11-03 10:59:39 CMG Hausa
Duk da kakkarfar adawa daga gida da waje, kamfanin samar da lantarki na 2 na Tokyo ko TEPCO dake kasar Japan, ya fara zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Fukushima cikin teku a zagaye na 3, aikin da ake fatan ci gaba da gudanarwa har zuwa ranar 20 ga watan nan na Nuwamba, kuma adadin ruwan da za a juye a wannan lokaci zai kai kusan tan 7,800.
Sai dai duk da haka, mako guda da ya gabata, kamfanin ya gamu da hadarin fitar birbishin “radioactive”, wanda ya jefa 2 daga cikin ma’aikatan kamfanin cikin hadari, aka kuma garzaya da su zuwa asibiti. Wannan lamari ya karyata ikirarin Japan, na cewa ruwan dagwalon da take zubarwa a teku ba shi da hadari, kuma bai dace a yi wasa da hadarin dake tattare da hadarin birbishin nukiliya dake cikin ruwan ba.
Bayan aukuwar wannan hadari, jami’an hukumar lura da sana’ar kamun kifi ta Fukushima, sun ce ba su da sauran kwarin gwiwa game da kamfanin TEPCO. Kaza lika rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai na nuna cewa, da yawa daga manyan jami’an kasar Japan da suka yi ritaya, suna aiki a kamfanin na TEPCO a matsayin masu ba da shawarwari, kuma wasu jami’ai dake aiki a sashen masana’antun nukiliyar kasar za su shiga gwamnatin ta Japan a matsayin rukunin masu ba da shawara.
Yanzu haka dai watanni biyu ke nan tun bayan da kasar Japan ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliyarta cikin teku. Sai dai abun da ya faru na hadari a baya bayan nan, ya tabbatar da bukatar da ake da ita, ta aiwatar da tsare tsaren sanya ido na kasa da kasa na dogon lokaci, kuma masu inganci.
Idan har da gaske ne kasar Japan tana da karfin gwiwa game da rashin hadarin wannan mataki nata, to kamata ya yi ta zubar da ruwan dagwalon bisa hangen nesa, kana ta goyi bayan kafuwar tsarin sanya ido na dogon lokaci, tare da halartar dukkanin masu ruwa da tsaki, ciki har da sanya ido daga sassa masu zaman kansu daga wasu kasashe.
Teku dai tamkar gida ne na bai daya ga daukacin bil Adama, kuma bai dace sauran sassan duniya su dauki alhakin son zuciyar kasar Japan ba. (Saminu Alhassan)