logo

HAUSA

Firaministan DR Congo ya kaddamar da cibiyar bayanai da Huawei ya gina

2023-11-03 10:42:01 CMG Hausa

A ranar Alhamis ne firaministan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC), Sama Lukonde Kyenge ya kaddamar da wata cibiyar bayanai a ma’aikatar kudi, da kamfanin Huawei na kasar Sin ya gina.

A cikin bayanin firaministan na Congo kafin ya kaddamar da cibiyar, wacce ta kasance ta farko a kasar, ya yaba da aikin inda ya ce, aikin na nuni da nasarar hadin gwiwa tsakanin DRC da kasar Sin, yayin da cibiyar bayanan za ta taka muhimmiyar rawa a ci gaban zamantakewar kasar.

Da yake godewa gwamnatin kasar Sin da bankin shigi da ficin kayayyakin kasar Sin, ministan kudi na kasar Congo Nicolas Kazadi ya ce, wannan cibiyar bayanai za ta sa kaimi ga zamanantarwa, da shugabanci na gari, da yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Zhao Bin, jakadan kasar Sin a DRC, ya bayyana cibiyar a matsayin "babbar nasarar hadin gwiwar Sin da Congo" a fannin samar da bayanai ta hanyar fasahar zamani. (Muhammed Yahaya)