logo

HAUSA

Nijeriya na tattaunawa da bangaren kasar Sin a bangarorin tsaro

2023-11-03 14:29:40 CMG Hausa

 

Ministan tsaron Nijeriya Badaru Abubakar, ya ce Nijeriya na goyon bayan hadin gwiwar kasa da kasa wajen neman sulhu da tattaunawar diflomasiyya  domin magance rikice-rikice da wanzar da zaman lafiya a duniya.

Badaru Abubakar ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da CGTN Hausa a yau Juma’a, yayin da yake tsokaci dongane da furucin kasar Sin a taron tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 10 cewa, a shirye take ta zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa domin tabbatar da tsaro a duniya.

Har ila ya yaba da taron na Xiangshan na Beijing karo na 10. Yana mai cewa ya bude kofar tattaunawa tsakanin kasa da kasa, inda aka yi tattaunawa masu muhimmanci ta yadda za a taimaki juna a fannonin tsaro. (Faiza Mustapha)