logo

HAUSA

Shanghai: an kammala dukkan shirye-shiryen CIIE karo na 6

2023-11-03 18:51:14 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barkanmu da war haka! Ya zuwa yau Jumma’a, an kammala dukkan shirye-shiryen da suka dace game da bude bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na 6 a birnin Shanghai, kuma bikin na bana zai kasance bikin baje koli mai tsafta maras gurbata muhalli.