logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a hada kai wajen samar da tsaron fasahar AI

2023-11-02 10:16:00 CMG Hausa

Tawagar kasar Sin dake halartar taron kolin kiyaye tsaron fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam (AI) dake gudana a Burtaniya, ta yi kira da a yi musayar ra'ayi da hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya kan batutuwan da suka shafi fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam da tafiyar da harkokin duniya.

Mataimakin ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wu Zhaohui, ya yi jawabi a yayin taron kolin da aka bude jiya Laraba, ita ma tawagar kasar Sin ta halarci taron tattaunawa kan yadda za a kiyaye tsaron fasahar da dai sauransu.

Tawagar kasar Sin a taron ta gabatar da shirin gwamnati kan fasahar kere-kere ta duniya da aka kaddamar a yayin taron dandalin hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na uku da aka gudanar a birnin Beijing ranar 18 ga watan da ya gabata, inda take fatan gudanar da shawarwari da kasashen da abin ya shafa.

Tawagar ta kuma jaddada cewa, taron ya samar da wani muhimmin dandali na tattaunawa, da damarmakin yin musaya da hadin gwiwa tsakanin kasashe, kan yadda za a samar da tsaro ga fasahar AI da tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Ta kuma yi imanin cewa, tafiyar da harkokin fasahar AI, na da tasiri kan makomar dukkan bil'adama, kuma wani nauyi ne da ya kamata kasashen duniya su magance shi. (Ibrahim Yaya)