logo

HAUSA

Sin ce ke rike da shugabancin kwamitin sulhun MDD a Nuwamba

2023-11-02 14:58:48 CMG Hausa

Kasar Sin ta karbi ragamar shugabancin kwamitin sulhu na MDD na watan Nuwamba daga ranar 1 ga watan. A wannan rana, Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya jagorancin shawarwarin cikin gida na kwamitin sulhu na majalisar, tare da amincewa da tsarin aikin kwamitin sulhu na wannan wata.

Zhang Jun ya bayyana cewa, halin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila shi ne batu mafi muhimmanci a ajandar kwamitin sulhu na wannan wata. Aiki mafi gaggawa shi ne karfafa maganar tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin, da hana karin asarar rayukan fararen hula, bala'o'in jin kai, da rikice-rikice. A matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na majalisar na wannan karo, kasar Sin za ta yi biyayya ga kiraye-kirayen kasashen duniya, da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa, wajen sa kaimi ga kwamitin don daukar matakai na bai daya masu ma'ana cikin lokaci. (Yahaya)