Wasan kwallon kwando na haskaka zukatan mazauna wani kauye dake lardin Guizhou
2023-11-02 21:23:21 CMG Hausa
Lu Dajiang dattijo ne mai shekaru 81 a duniya, ya kuma fara wasan kwallon kwando ne tun yana dan shekara 7 da haihuwa, kuma har yanzu yana zuwa filin wasan kwando na kauye su domin taba wasa.
Lu dan asalin kauyen Taipan dake gundumar Taijiang ta lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin ne, kuma kauyen su na da yawan jama’a sama da 1,100 cikin iyalai sama da 270. Kaza lika kaso 2 bisa 3 na jama’ar kauyensu na sha’awar kwallon kwando.
Yayin bikin gargajiya na Chixin, wanda ke gudana a ranar 6 ga watan 6 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, jama’ar kauyen su Lu na gudanar da gasar kwallon kwando, inda suke gayyatar mutanen garuruwan dake kusa da su domin halartar bikin murnar samun girbi mai yalwa.
Ko shakka ba bu wasan kwallon kwando ya samu matukar karbuwa tsakanin al’ummun wannan kauye a tsawon sama da shekaru 80, inda suke mika gadon wannan wasa daga zuri’a zuwa zuri’a.
Wu Xiaolong, mazaunin wannan kauye ne da aka Haifa bayan shekarar 1990, ya fara wasan kwallon kwando tun yana da shekaru 10, kuma ya kan gayyaci sa’o’in sa domin su buga wasa tare, ya ce yayin da yake kara girma, yana kuma kara sha’awar wannan wasa. Sha’awar sa ga kwallon kwando ta karu zuwa matukar kaunar wasan, yayin da wasan ya sauya mahangarsa ta rayuwa.
Bayan ya kammala makarantar karamar sakandare, Wu ya kusa gaza samun sakamako mai kyau na ci gaba da karatu, inda har ya fara shirin tafiya neman aikin yi. Bisa umarnin iyayen sa da kuma damar da zai samu ta ci gaba da buga wasan kwallon kwando, Wu ya ci gaba da karatu, ya kuma samu nasarar zama daya daga mambobin kungiyar kwallon kwando ta babbar sakandare da ya shiga.
A shekarar 2011, Wu ya samu shiga jami’a. Kuma bayan kammalawa ya zama mai horas da dalibai wasannin motsa jiki a makarantar firamaren garin su. Baya ga aikin koyarwa, Wu yana kuma baiwa dalibai sama da 50 horo, bayan an tashi daga makaranta.
Wu ya ce a can baya, yana buga kwallon kwando ne kawai ta hanyar koyo daga masu bugawa, amma a yanzu yaran da yake horaswa sun samu damar koyo daga kwararru. Ya ce yana alfahari da damar da ya samu ta taimakawa yaran da dabarun inganta wasan kwallon kwando, kuma yana da burin ganin yaran sun cimma nasarar mafarkin su.
A kauyen Taipan, a duk lokacin da aka fara buga kwallon kwando, matasa dake waje na gaggawar hada kan su waje guda domin su shiga a buga tare da su. A yanzu, Wu yana alkalancin wasan, yana kuma yin aikin bayanin yadda wasan ke gudana, karkashin kungiyar kwallon kwando ta garin su.
A cewar sa "Na ji dadin lokacin samartaka saboda kwallon kwando. Ina sha’awar raba wannan nishadi da jin dadi da na samu ta kwallon kwando tare da al’umma ta".
Sakamakon zuwan lokacin biki, da kuma kyakkyawan yanayin wannan kauye na su Wu, kwallon kwando da ake bugawa a kauyen ta samu karbuwa matuka tsakanin masu kallo ta yanar gizo, inda har ta kai wasan yana jan hankalin ‘yan wasan kwallon kwando na kasa da kasa.
A watan Yulin bana, shahararren dan wasan kwallon kwando na NBA Jimmy Butler, ya ziyarci kauyen Taipan domin karrama bikin da ya gudana.
Li Jiahao, yaro ne mai shekaru 14 daga kabilar Miao a kauyen Taipan, wanda a yanzu yake halartar makarantar birnin Yunfu dake lardin Guangdong, sakamakon kaura da iyayen sa suka yi zuwa can domin aiki. A can gida, Li ya yi suna wajen kwallon kwando, ya kuma roki mahaifin sa da ya ba shi damar shiga gasar da aka shirya yayin bikin Chixin. Kuma abun mamaki sai ga shi Li ya hadu da tauraron sa a yayin wannan gasa.
Li ya ce "A matsayina na dan wasa dake matakin farko, ina iyakacin kokari wajen ganin ban karaya ba, yayin da ake buga wasa mai cike da kalubale. Fata na shi ne na yi karfi, da kwarewa kamar Jimmy Butler, kuma na cimma burika na a karatu da rayuwa".
A ranar 25 ga watan Oktoba, ranar da aka buga wasan karshe na gasar kwallon kwando ta kauyen Taipan, wadda aka yiwa lakabi da gasar CunBA, an fafata tsakanin kungiyoyi 8, daga sassa daban daban na kasar Sin.
Tun daga kauyen da ya sauki bakin gasar, har zuwa kungiyoyin larduna dake fafatawa, wannan kauye mai tsaunuka ya samar da gasanni dake hallara sassan ‘yan wasa na kasa baki daya.
A cewar dattijo Lu Dajiang mai shekaru 81 a duniya, “Ganin tarin ‘yan wasa dake buga kwallo a filin wasa, ya sa ni sha’awar shiga a buga tare da ni. Har yanzu ina ajiye da rigar wasa na ta kungiyar gida wadda a baya nake wasa sanye da ita. Ina jin dadin lafiyar jiki da na samu ta hanyar wasa, ina kuma fatan kara buga wani wasan idan an bani dama.