logo

HAUSA

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza

2023-11-02 11:08:36 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi na ganin an tsagaita bude wuta na jin kai, Isra'ila ta ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza mai yawan jama'a a jiya Laraba, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani babban kwamandan kungiyar Hamas, a wani harin da ta kai ta sama, yayin da rukunin farko na mutanen dake barin yankin suka shiga Masar, tun bayan rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Hamas a ranar 7 ga Oktoba.

Wasu majiyoyi daga bangarorin Masar da Palasdinawa na cewa, a jiya ne kuma, rukunin farko na masu rike da fasfo na kasashen waje kimanin 500,da kuma wasu mutane 80 da suka jikkata, suka shiga Masar ta mashigar kan iyakar Rafah, hanya daya tilo ga wadanda ke neman barin yankin da rikicin ya daidaita

A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, ya zuwa yanzu, adadin Falasdinawa da aka kashe a Gaza, ya kai a kalla 8,796, wadanda suka hada da yara 3,648 da mata 2,290. A yammacin kogin Jordan da aka mamaye kuwa, sama da Falasdinawa 132 ne sojojin Isra'ila da Yahudawa mazauna wurin suka kashe.

A bangaren diflomasiyya, Bolivia ta yanke huldar diflomasiyya da Isra'ila, saboda yawan  Falasdinawa da aka kashe a Gaza. A halin da ake ciki kuma, kasashen Jordan, da Chile, da Colombia, sun janye jakadansu dake Isra’ila.

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran, jiya Laraba ya bukaci gwamnatocin kasashen musulmi, da su hada kai tare da dakatar man fetur da sauran kayayyakin da ake fitarwa zuwa Isra'ila, don matsawa mata lamba ta dakatar da hare-haren da take kaiwa kan Gaza. (Ibrahim)