logo

HAUSA

Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa

2023-11-02 15:37:58 CMG Hausa

Yayin da baje kolin kasa da kasa na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 6 ke kara karatowa, yanzu haka sassan ’yan kasuwa, da masu ruwa da tsaki a hada hadar cinikayya daga bangarorin kasashen duniya daban daban, na kara nuna fatansu na halartar wannan muhimmin biki, ciki har da sassa da dama daga kasashen Afirka.

A baya bayan nan ma, wata tawaga karkashin hukumar yayatawa, da bunkasa cinikayya ta kasar Zimbabwe mai lakabin “ZimTrade”, ta bayyana shirya ta na halartar wannan baje koli, kunshe da wakilai daga kamfanoni sama da 15.

To ko me ya sa bikin baje kolin na CIIE dake gudana a birnin Shanghai, wanda kuma a bana za a yi tsakanin ranaikun 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba ke jan hankalin ’yan kasuwa, da sauran masu ruwa da tsaki? Ko shakka babu amsar wannan tambaya shi ne tagomashin da bikin ke da shi ta fuskar samar da babbar dama, ta yin cudanya, da karfafawa ko kulla sabbin alakokin cinikayya tsakanin mahalartansa.

Baje kolin na CIIE ya zamo wani babban dandali na baiwa ’yan kasuwa damar gano abubuwan da babbar kasuwar kasar Sin ke bukata, da zakulo damammakin cinikayya masu inganci ga dukkanin sassa.

Ga tawagar “ZimTrade” ta kasar Zimbabwe, a wannan karo ta shirya zuwa baje kolin na CIIE tare da wakilan kamfanonin sarrafa fatu, da na na sarrafa abinci, da masu sana’o’in fasahohin hannu, da kamfannonin sadarwar tarho, da na hakar ma’adanai. Sauran su ne na makamashi da kuma na yawon bude ido.

Masharhanta na kallon baje kolin na wannan karo a matsayin wata dama, ta yaukaka alakar cinikayya tsakanin Sin da Zimbabwe, wadda a baya bayan nan ke kara fadada, inda ta kai kasar Sin din zama ta uku mafi karbar hajojin da Zimbabwe ke fitarwa ketare cikin shekaru 3 da suka gabata.

Baje kolin CIIE, ya ci gaba da kasance muhimmin dandali na kyautata fahimtar juna tsakanin ’yan kasuwa, kasancewarsa mafi girma a fanin baiwa masu ruwa da tsaki damar nazartar tsarin Sin na kara bude kofa ga waje, da shigar da hajoji cikin babbar kasuwar kasar ta Sin. (Saminu Alhassan)