logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a rikicin Isra’ila da Hamas ya zarce 10,000

2023-11-02 20:23:24 CMG Hausa

 

Wasu majiyoyi daga Palasdinu da Isra’ila sun bayyana cewa, adadin wadanda suka mutu sanadiyyar rikicin Isra’ila da Hamas ya zarce 10,000, tun bayan da rikicin ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, yanzu haka, adadin Palasdinawan da suka mutu sakamakon rikicin a Gaza ya kai akalla 8,796, ciki har da yara 3,648 da mata 2,290, yayin da sama da 1,400 suka mutu a Isra’ila, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila.

Akalla ‘yan kasashen waje 320 da gomman mutanen Gaza da suka jikkata ne suka tsallaka Masar ta mashigar iyakar Rafah a jiya Laraba a rukuni na farko, karkashin wata yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Masar da Hamas. (Fa’iza Mustapha)