logo

HAUSA

Yaya za a cimma “tsaro tare”? Dandalin Xiangshan ya gabatar da wasu tunani

2023-11-01 13:46:46 CMG Hausa

An rufe taron dandalin tattaunawa kan batun tsaro na Xiangshan karo na 10 a birnin Beijing jiya Talata. Yayin taron, wakilai fiye da 1800 daga kasashe da yankuna da kuma kungiyoyin kasa da kasa sama da 100 sun gudanar da tattaunawa tare da musayar ra’ayoyi bisa taken “Tsaro na bai daya, zaman lafiya mai dorewa”, adadin mahalarta taron da mukamansu duka sun kai wani matsayin da ba a taba gani a da ba.

Yaya za a cimma buri na “tabbatar da tsaro tare”? Ta hanyar tattaunawar da aka yi a dandalin Xiangshan na Beijing, an samu kyakkyawar fahimta.

Ko shakka babu, manyan kasashe suna da nauyi da muhimmanci na musamman wajen wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A yayin taron, Xanthi Carras, direktar sashen kula da harkokin kasar Sin a ofishin mai ba da taimako ga mataimakin sakataren ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta halarci taron a madadin ma’aikatar tsaron kasar Amurka. 

Ana sa ran cewa, bangarorin Amurka da Sin za su iya kai zuciya nesa su yi kokarin samar da wani kyakkyawan yanayi, ta yadda za a iya tabbatar da ganin dangantakar dake tsakanin rundunonin soja na kasashen biyu ta samu ci gaba cikin kwanciyar hankali kamar yadda ake fata.

Idan ana son cimma buri na “tabbatar da tsaro tare”, abu mai muhimmanci shi ne tsayawa tsayin daka kan warware sabani da rikici dake kasancewa tsakanin kasa da kasa ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna cikin lumana. A wannan dandalin, an gayyaci wakilan wasu bangarorin da suke yin rikici da juna, kamar wakilan Isra'ila da na kasashen Larabawa, da Rasha da Ukraine don yin tattaunawa da tuntubar juna fuska da fuska.

Har yanzu, wasu manyan kasashen yamma suna bin ra’ayinsu na tabbatar da “cikakken tsaron kansu”, har ma suna bin tunanin yakin cacar baki, da kuma haddasa fito na fito tsakanin bangarori daban daban, da kuma haifar da kalubale mai sarkakiya ga yanayin kasa da kasa. Masana mahalarta taron suna ganin cewa, dandalin Xiangshan ya ba dukkan kasashen yammacin duniya damar sani da kuma fahimtar matsayi da ra'ayoyi daban daban na sauran kasashen duniya. Hakan yana da matukar muhimmanci ga kasashen duniya da su yi kokarin yin hadin gwiwa domin samun nasara tare. (Safiyah Ma)