logo

HAUSA

A kalla kamfanonin Sin 30 ne za su halarci bikin makon samarwa da tallata tufafi na Afirka

2023-11-01 09:56:38 CMG Hausa

A kalla kamfanoni 30 na kasar Sin ne ke shirin halartar bikin makon samarwa da tallafa tufafi na Afirka karo na 9 (ASFW). Bikin da zai gudana daga ranar 3 zuwa 6 ga watan Nuwamba a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, a cewar mashirya bikin.

Shugaban kungiyar masu samar da yaduna da tufafi na kasar Habasha, Goshu Negash ya bayyanawa taron ganawa da manema labarai cewa, bikin baje kolin na kasa da kasa na kwanaki hudu, zai hallara masu fitar da kayayyaki sama da 300, a fannonin sana’o’in adon yadi da tufafi da fata da fasaha da kuma adon gida. Yana mai cewa, a kalla 30 daga cikin masu baje kolin, sun fito ne daga kasar Sin.

Babban jami'in gudanarwa na cibiyar bayar da shawarar kasuwanci da baje koli (Gmbh) Skander Negasi, wadda ke cikin masu shirya baje kolin na shekara-shekara, ya ce kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannin samar da yaduna da ci gaban fasaha a fadin Afirka. Yana mai cewa, za su nuna dukkan wadannan a baje kolin tare da masu baje koli da za su zo daga kasar Sin. (Ibrahim Yaya)