logo

HAUSA

Kyawawan manufofin tattalin arzikin Sin na kara karfafawa kamfanonin ketare gwiwar shiga babbar kasuwar kasar

2023-11-01 17:25:07 CMG Hausa

A kwanakin baya ne rahoton taron dandalin tattauna harkokin kudi na duniya (IFF) ya sanar da cewa, ana sa ran GDPn kasar Sin zai bunkasa da kaso 5.2 a bana, da kuma kaso 5 a shekarar 2024.

Wannan na zuwa ne a gabar da wasu makiya a kwanakin baya ke yada bayanai marasa tushe game da tattalin arzikin kasar ta Sin, har ma ya sa babban bankin duniya ya fito da bayanan hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya, inda a cikinsa ya yi hasashen cewa, a bana tattalin arzikin Sin zai bunkasa da kaso 5.6 cikin 100, yayin da OECD kuma ya yi hasashen bunkasar za ta kai kaso 5.4, shi kuma asusun bayar da lamuni na duniya (IMF), ya yi hasashen karuwar zuwa kaso 5.2 cikin 100.

Masu sharhi na cewa, kwanciyar hankali da dorewar manufofin tattalin arzikin Sin, sun karfafa gwiwar kamfanonin duniya kara shiga babbar kasuwar kasar. Sun kuma yi imanin cewa, kasar Sin tana daya daga cikin manyan kasashe a duniya dake samar da damammakin ci gaba ga kamfanonin kasa da kasa.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya an fitar da alkaluman kididdigar tattalin arzikin kasar Sin, wanda ke nuna karuwar hajoji da kayayyakin masarufi da ta sayar. Wannan ya kara tabbatar da cewa, alkaluman tattalin arzikin Sin sun inganta kuma cinikayyar hajojin kasar ta zarce yadda ake zato.

Baya ga wadannan alkaluma, akwai kuma damammaki na yin kasuwanci da baki daga waje ke matukar sha’awa. Tun daga farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya yake fuskantar tafiyar hawainiya, kuma sakamakon durkushewar wasu manufofi a manyan kasashe masu karfin tattalin arziki shi ma ya fito fili.

Abin farin ciki shi ne, tattalin arzikin kasar Sin ya jure matsin lamba, ya kuma ci gaba da farfadowa, kuma yana ci gaba da zama wani muhimmin inji na bunkasar tattalin arzikin duniya. Lamarin dake kara baiwa ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya karfin gwiwa da sha’awar kara shiga babbar kasuwar kasar don gudanar da harkokin kasuwanci da samun riba mai gwafi. (Ibrahim Yaya)