logo

HAUSA

CIIE: Wani muhimmin dandalin zuba jari da saye da sayarwa na duniya

2023-11-01 07:55:03 CMG Hausa

Yanzu haka shirye-shirye sun yi nisa, don gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 6 (CIIE) a birnin Shanghai na kasar Sin, bikin da za a bude a ranar 5 har zuwa 10 ga watan Nuwanban wannan shekara.

Bikin baje kolin na CIIE, wani bangare ne na manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen ketare, da tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, da kokarin mai da ci gaban kasar damar raya tattalin arzikin duniya.

A matsayinsa na bikin baje kolin kasa da kasa na farko a duniya, bikin na CIIE ya kasance wani muhimmin dandali na saye da sayarwa na kasa da kasa, da inganta zuba jari da musaya tsakanin al’ummomi da na al’adu, da hadin gwiwar dake shafar kowa da kowa tun lokacin da aka fara gudanar da shi a shekarar 2018. 

Alkaluma na nuna cewa, yayin bukukuwan CIIE guda 5 da aka gudanar a baya, yawan darajar kwangilolin da aka kulla ta kai dalar Amurka biliyan 272.3. Masu sharhi na fatan bikin baje kolin wannan karo, zai kara janyo hankalin dukkan sassa masu ruwa da tsaki.

Kamar yadda ta sha bayyanawa, kasar Sin za ta ingiza burin dukkan kasashen duniya na cin gajiya daga damammakin babbar kasuwar kasar, da moriyar dake tattare da kara bude kofar kasar, da zurfafa hadin gwiwar sassan kasa da kasa. Don haka, manufar kasar Sin ta bude kofa, ba kasar kadai za ta amfana ba, har ma da ragowar kasashen duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)