logo

HAUSA

Aikin shimfida bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kano ya ci kaso 80 na kammaluwarsa

2023-11-01 11:20:49 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yaba da kokarin kamfanin Brentex CPP mallakin ’yan kasuwar kasar Sin bisa himmar da yake nunawa a aikin shimfida bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kano wanda yanzu haka aikin ya ci kaso 80 na kammaluwarsa.

Babban manajan daraktan gungun kamfanin mai na kasa NNPCL Malam Mele Kyari ne ya yi yabon lokacin da manyan jami’an kamfanin suka kai ziyarar gani da ido bangaren kashi na 2 na aikin dake yankin Tamburawa a jihar Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Malam Mele Kyari wanda ya samu wakilcin Mr Olalikon Ogunlaye ya ce, bisa yadda akin ke gudana, akwai hasken cewa wa’adin da aka baiwa kamfanin na Brentex wajen kammala aiki a shekara ta 2024 zai iya cimmawa.

Kashi na biyu na aikin ya kunshi shimfida bututun iskar gas mai tsawon kilomita 320 tare kuma da gina tashoshi a wasu kebantattun wurare.

“Aikin shimfida bututun gas din zai kara samar da bunkasar arziki, zai kuma baiwa masana’antu damar ci gaba, sannan al’ummar za su samu yalwa, sakonnin shugaban kasa da babban manajan daraktan kamfanin na NNPC a bayyane suke, wajibi ne a mayar da hankali wajen tabbatar da aiki na-gari kuma mai karko domin ’yan Najeriya su ci gajiyarsa.”

Da yake nasa jawabi, shugaban kamfanin na Brentex CPP Ltd, Mr Wang Hao ya jaddada cewa, a shirye kamfaninsa yake ya gudanar da ayyuka masu inganci ga gwamnatin Najeriya.

Ya ce, kamfanin ya samar da damarmakin aikin yi ga ’yan kasa.

“A kalla mun dauki kananan ma’aikata da suke zaune a kewayen da muke gudanar da wannan aiki har su dari 7 wadanda suka hada da leburori da sauran wadanda suke da kwarewa ta musamman.”

Mr Wang ya yi alkawarin cewa kamfanin na Brentex CPP zai kammala aikin kwangilar a kan lokaci kamar yadda yake a daftarin yarjejeniyar aikin. (Garba Abdullahi Bagwai)