logo

HAUSA

Masar ta karbi Palasdinawan da suka jikkata ta mashigar Rafah

2023-11-01 20:59:39 CMG Hausa

 

Kasar Masar ta karbi Palasdinawan da suka jikkata daga zirin Gaza da aka yi wa kawanya ta mashigar Rafah a yau Laraba. Mashigar Rafah ita ce kadai hanyar da ta hada Masar da zirin Gaza.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an garzaya da wasu mutane 5 da suka jikkata zuwa asibitin Arish dake arewacin yankin Sinai.

Majiyar ta kara da cewa, jimilar mutane 81 da suka jikkata ne za su shiga Masar a yau Laraba, cikin kashi na farko.

Har ila yau, kusan ‘yan kasashen waje 500 ne za su tsallaka zuwa Masar, bayan shigar wadanda suka jikkata. (Fa’iza Mustapha)