logo

HAUSA

Me ya hana Amurka ta ce “A tsagaita bude wuta”?

2023-11-01 22:19:45 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

John Kirby, babban jami’in kwamitin kula da harkokin tsaro na fadar White House ya bayyana a gun wani taron manema labarai da aka gudanar a kwanan baya cewa, a ganin Amurka, tsagaita bude wuta, ba ita ce hanyar da ta dace ta daidaita batun Palasdinu da Isra’ila ba, don haka, ba ta fatan ganin an tsagaita bude wuta nan da nan. Ya kara da cewa, Isra’ila na ci gaba da daukar matakai na yakar manyan jami’an Hamas, kuma a ganin Amurka, kungiyar Hamas ita ce kadai ke iya amfana daga tsagaita bude wuta. Sai kuma a makon da ya gabata, mista Kirby ya ce, yanzu lokaci bai yi ba na tsagaita bude wuta a zirin Gaza.

Sama da mutane dubu 10 na Palasdinu da Isra’ila sun halaka a rikicin da ya barke a tsakaninsu a wannan karo. Amma abin takaici shi ne tun bayan barkewar rikicin, shugaban kasar Amurka da sauran manyan jami’an kasar, duk sun yi shiru game da batun tsagaita bude wuta. Daftarin kudurin da Amurka ta gabatar ga kwamitin sulhu na MDD ma bai yi bayani a kan batun tsagaita bude wuta ba, baya ga haka, Amurka ta jefa kuri’ar nuna rashin amincewa da kudurin da aka zartas a babban taron MDD, wanda ya yi kira da a tsagaita bude wuta a tsakanin Palasdinu da Isra’ila.

Ke nan me ya hana Amurka ta ce “A tsagaita bude wuta”, a yayin da ake fuskantar wannan mummunan rikicin zubar da jini?

A hakika, huldar dake tsakaninta da Isra’ila na da muhimmiyar ma’ana gare ta. Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya taba bayyanawa a jawabin da ya gabatar a shekarun da suka gabata cewa, “Da a ce babu Isra’ila, to Amurka za ta kirkiro Isra’ila, don kare muradunta a yankin gabas ta tsakiya.” Kasancewar Isra’ila kasa ce mai karfi ta fannin soja da leken asiri, Amurka na daukarta a matsayin babban makaminta a yankin gabas ta tsakiya, abin da ya sa Amurka ta dade tana nuna goyon baya ga Isra’ila. A sa’i daya kuma, a kan ce babu wanda zai ci nasara daga yaki, amma abin ba haka ba ne ga masana’antun samar da makamai na kasar Amurka. Kwana uku kadai bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, farashin hannayen jari na kamfanin Lockheed Martin ya karu da kaso 9%, a yayin da farashin ya karu da kashi 4% ga kamfanin Raytheon, wadanda ke daga cikin manyan kamfanonin samar da makamai biyar na kasar Amurka. Kamar yadda Greg Hayes, babban jami’in kamfanin Raytheon ya bayyana a yayin zantawa da ’yan jarida a kwanan baya cewa, “yaki abu ne na bakin ciki, amma yana kawo mana cinikin makamai.”

Rikici na ci gaba, a yayin da kuke karanta wannan sharhi, ya yiwu karin fararen hula sun mutu ko jikkata. Amma duk wadannan ba abu ne dake gaban muradunta ba, kuma “hakkin dan Adam” da ke bakinta ya zama banza a gaban muradunta. (Mai Zane: Mustapha Bulama)