logo

HAUSA

Yara da ke zirin Gaza

2023-11-01 11:36:21 CMG

Yara da ke zirin Gaza ke nan, wadanda rikicin da ke tsakanin Palasdinu da Isra’ila ke addabarsu. Alkaluman da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar sun shaida cewa, yara sama da 3500 sun mutu sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Palasdinu da Isra’ila na wannan karo. A cewar asusun kula da yara na MDD (UNICEF), yanzu haka yara kimanin miliyan daya na matukar bukatar kariya cikin gaggawa a zirin Gaza.