Dahiru Muhammad Hashim: Kiyaye muhalli na da muhimmanci sosai ga rayuwar dan Adam
2023-10-31 15:52:25 CMG Hausa
Dr. Dahiru Muhammad Hashim, dan Kano ne mai rajin kiyaye muhallin halittu, kana shugaban hukumar KN-ACReSAL da gwamnatin jihar Kano ta tura zuwa kasar Sin kwanan nan don halartar darussan horo kan dabarun magance sharar roba da ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin ta shirya, musamman ga kasashe masu tasowa.
A zantawarsa da Murtala Zhang, malam Dahiru Hashim ya bayyana yadda aka shirya musu darussan horo a kasar Sin, musamman a birnin Suzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar, gami da yadda Suzhou din ya burge shi a fannin tsabtar muhalli.
Ya kuma bayyana burinsa na ci gaba da fadakar da al’umma kan muhimmancin kiyaye muhalli. (Murtala Zhang)