logo

HAUSA

Tsaro Shi Ne Kashin Bayan Ci Gaban Kowacce Kasa

2023-10-31 16:39:33 CMG Hausa

An kaddamar da babban taron tattauna batutuwan tsaro na kasa da kasa na Xiangshan karo na 10, jiya Litinin a birnin Beijing. Tabbas batun tsaro muhimmin batu ne da ya shafi kowacce kasa da yanki da kuma duniya, domin shi ne kashin bayan samun ci gaban da ake muradi.

Sauye-sauyen da bil adama ke gani a wannan zamani, kama daga ayyukan ta’addanci da juyin mulki da yake-yake da fito-na-fito, abubuwa ne da aka dade ba a gani ba, wanda kuma bai kamata a ce ana fama da su a wannan zamani na wayewar kai ba.

Lamuran dake faruwa a baya-bayan nan sun nuna cewa, babu wanda zai iya tsira daga irin wadannan matsaloli, don haka, ya dace kasashe su tashi tsaye domin daukar dabarun dakatar da faruwarsu, ta hanyar tattaunawa da musayar ra’ayi da hadin gwiwa da koyi da dabarun juna.

A baya-bayan nan, kudurin neman tsagaita bude wuta a rikicin Falasdinu da Isra’ila ya samu kuri’un amincewa mai yawa a MDD, lamarin da ya nuna cewa kasashen duniya suna da ra’ayi na bai daya kan samun zaman lafiya a duniya. Sai dai, abin takaici shi ne, duk da haka, akwai wadansu tsiraru dake cin gajiyar rikice-rikicen, inda suke yin biris da matsalolin da suka addabe su a cikin gida, suke kara rura wutar rikici tsakanin kasa da kasa

Kamar yadda mataimakin shugaban rundunar sojin kasar Sin janar Zhang Youxia ya bayyana a jawabin bude taron Xinagshan, dole ne kasashen duniya su farga game da karuwar rikice-rikice, da fito-na-fito. A ganina, dabarar yin hakan ita ce, hadin gwiwa da girmama juna da tattaunawa, a don haka nake ganin wannan taro ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa.

Kasar Sin mai masaukin baki, ta bayyana cewa, a shirye take ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa kan tsaro da karfafa tsarin tsaro na duniya. Kowa zai iya shaidar kasar Sin wajen nuna dattako da kai zuciya nesa. Wannan ya tuna min da furucin da mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya yi a kwanakin baya yayin zantawarsa da sashen Hausa na rediyon kasar Sin cewa, Sin ba ta taba kai hari ba, kuma tana kaunar zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Yayin da muke kara shaidawa da fahimtar yanayin da duniya ke cika, dole ne kasashenmu su yi koyi da Sin, su kasance masu kaunar zaman lafiya da hadin gwiwa da tuntuba da girmama juna, domin samun zaman lafiya da ci gaban da al’ummar duniya ke muradi. (Fa’iza Mustapha)