logo

HAUSA

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta kasa a Gaza

2023-10-31 11:01:22 CMG Hausa

Rahotanni na cewa, sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai farmaki ta kasa a zirin Gaza jiya Litinin, yayin da adadin wadanda suka mutu a yankin da aka yiwa kawanya, ya zarce dubu 8 da 300.

A jiyan ne kuma, rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, an sako wani sojan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da shi a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma yana cikin koshin lafiya. Tana mai jaddada cewa, za ta ci gaba da daukar duk wani mataki, don ganin ta dawo da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

A halin da ake ciki kuma, wani jami'in Hamas ya musanta ikirarin sojojin na Isra'ila, yana mai cewa sanarwar da rundunar ta bayar na kwato sojan nata, wani yunkuri na haifar da rudani kuma babu wanda ya yarda da labarin Isra'ila.

Duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi na neman tsagaita bude wuta a Gaza da kuma sakin fararen hula da ake tsare da su, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya fada a yammacin jiya cewa, babu batun tsagaita bude wuta.

A cewar kamfanin dillancin labaran Palasdinawa (WAFA), adadin Palasdinawan da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, ya karu zuwa 8,382, yayin da fiye da mutane 1,400 suka rasa rayukansu a bangaren Isra’ila, mafi yawa a harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda shi ne ya haifar da rikici na baya-bayan nan. (Ibrahim)