logo

HAUSA

UNECA: Samun wadatar abinci da makamashi shi ne jigon tabbatar da muradun SDGs a Afirka

2023-10-31 09:31:35 CMG Hausa

Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (UNECA) ta bayyana cewa, nasarar samar da abinci da makamashi, abu ne mai muhimmanci wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa na MDD (SDGs) a Afirka.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta UNECA ta fitar ta bayyana cewa, yayin da tattalin arzikin duniya ke ci gaba da fama da tasirin annobar COVID-19, da kuma illar rikicin kasashen Rasha da Ukraine, kan farashin abinci da makamashi, samun nasarar samar da abinci da makamashi, na da matukar muhimmanci ga kasashen Afirka, musamman yankunan arewaci da yammacin nahiyar.

A cewar hukumar, tasirin cutar COVID-19 da rikicin Rasha da Ukraine, na kara yawan kudaden da ake ranta da ma ruwan lamuni a Afirka, wanda hakan ke kara ta’azzara, sakamakon rashin daidaituwar tasirin sauyin yanayi da ke shafar kashi 2 zuwa 9 na kasafin kudaden kasashen Afirka.

Ta ce, sakamakon rikice-rikicen da ake fama da su, an fuskanci gagarumin koma baya, a kokarin da ake na samar da abinci da makamashi a yankunan arewaci da yammacin Afirka. Alkaluman hukumar ta UNECA sun nuna cewa, tsakanin shekarar 2019 zuwa ta 2022, kusan karin mutane miliyan 25 ne, suka yi fama da rashin abinci mai gina jiki a yankunan biyu. (Ibrahim)