logo

HAUSA

IOC ya amince da sanya karin wasanni 5 cikin jerin wasannin da za a fafata a gasar Olympics ta Los Angeles a 2028

2023-10-30 15:40:08 CRI

Bayan zaman hukumar shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kaso ko IOC karo na 141, hukumar ta amince da sanya wasannin Cricket, da baseball cikin jerin wasannin da za a fafata a cikin su, yayin gasar Olympic ta birnin Los Angeles na Amurka a shekarar 2028. Baya ga Cricket da baseball, an kuma amince da sanya wasannin Flag football, da lacrosse da squash, cikin jerin sabbin wasannin da za a fafata cikin su. An amince da wasannin 5 ne yayin kuri’ar da aka kada, ko da yake cikin duk kuri’u 90 akwai kimanin biyu na nuna rashin amincewa.

Hukumar IOC ta ce kwamitin ta mai aikin shirya gasar Los Angeles ta 2028 ne ya gabatar da shawarar kara wasannin 5, kuma za a gudanar da su ne kadai a gasar ta 2028, kana sashen tsara gasanni na hukumar ya nazarci shawarar kafin gabatar da ita ga majalissar manyan jami’an IOC.

Wasannin baseball, da cricket da lacrosse, da ma sun taba kasancewa cikin wasannin da aka taba yin su a Olympic, ciki har da wanda aka gudanar a birnin Tokyo a shekarar 2020, yayin da wasannin flag football da squash, wannan ne karon farko da za a gudanar da su a gasar Olympic ta birnin Los Angeles.

Gasar Olympic ta LA 2028, za ta kasance ta farko da za a fafata wasan cricket a cikin ta, tun bayan gasar ta shekarar 1900 ta birnin Paris, yayin da wasan lacrosse zai shiga gasar Olympic a karo na 3, bayan fafatawa a gasar a shekarun 1904 a St. Louis, da gasar London ta shekarar 1908.

Wasannin Cricket da baseball za su dawo cikin wasannin Olympic ta birnin Los Angeles a shekarar 2028, bayan amincewar hakan da IOC ta nuna.

Da yake tsokaci kan wannan ci gaba, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach, ya ce "Amincewa da kara wasannin 5 cikin wadannan da za a rika fafatawa yayin gasar Olympic ta Los Angeles a 2028, ya dace da al’adar wasannin Amurka, kuma matakin zai gabatarwa duniya yanayin wasanni irin na Amurka, da gabatarwa Amurka nau’o’in wasannin kasa da kasa. Wadannan wasanni 5 da aka kara za su zamo na musamman ga gasar Olympic ta LA ta 2028. Kaza lika kara wasannin 5 zai baiwa gasar Olympic din damar cudanya da sabbin ‘yan wasa, da sauran masu sha’awar wasanni dake Amurka da ma sauran sassan duniya".

A nasa tsokaci kuwa, shugaban kwamitin shirya gasar LA 2028 Casey Wasserman, ya ce "Na jima da amincewa, cewa akwai babbar dama ta samun nasara shirya gasa mai kayatarwa a Los Angeles, ba wai gare ku kadai ba, har ma ga dukkanin duniya baki daya. Dukkanin tsare-tsaren mu na Olympic na nuni ga hakan. Muna farin ciki da damar kawo sauyi ta hanyar yin hadin gwiwa da manyan hukumomin shirya gasanni, wanda hakan zai bude kofofin damammaki masu yawa, ta yadda za mu daga matsayar Olympic, da ajin gasar na masu bukata ta musamman, da janyo ra’ayin sabbin masu sha’awar wasanni”.

Yayin wata kuri’ar ta daban, mambobin IOC sun tabbatar da cewa, wasannin daga nauyi, da rukunin wasannin pentathlon na zamani, mai kunshe da wasannin harbin bingida, da tseren doki, da wasan gudu, da linkaya, da wasan fadan takobi, duk za su ci gaba da kasancewa cikin wasannin gasar Olympic, bayan da hukumar lura da wasannin daga nauyi ta IWF, ta dauki matakan shawo kan matsalolin shan magungunan kara kuzari. A hannu guda kuma, a bangaren rukunin wasannin pentathlon na zamani, an maye gurbin wasan tsallake shinge da dawaki, da wasan tsere da tsallake shinge.

Baya ga wasannin da muka ambata, an kuma dakatar da sanya wasan damben boxing cikin wasannin da za a fafata a gasar ta LA 2028, kasancewar IOC bai kai ga amincewa da wata hukuma mai alhakin jagorantar wasan boxing na Olympic ba, tun bayan da IOCn ya yanke hukuncin janye amincewar da ya yiwa hukumar “International Boxing Association ko IBA.