logo

HAUSA

A kalla mutane 10 sun rasu sakamakon hadarin jirgin kasa a Indiya

2023-10-30 11:14:06 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Indiya na cewa a kalla mutane 10 sun rasa rayukan su, kana wasu 25 sun jikkata da yammacin jiya Lahadi, sakamakon hadarin jirgin kasa da ya rutsa da su a jihar Andhra Pradesh dake kudancin kasar. 

Kamfanin dillancin labaran kasar PTI, ya ce wasu jiragen kasa biyu ne suka yi taho mu gama, tsakanin yankin Alamanda da Kantakapalle na arewacin jihar ta Andhra Pradesh, kuma hadarin ya faru ne sakamakon kin tsayawar da daya daga jiragen ya yi a wurin da aka umarce shi.  

Firaministan kasar Narendra Modi, ya wallafa wani sako a shafin X, wanda a baya ake kira Tiwita, wanda ke cewa ya zanta da ministan sufurin jiragen kasa, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su sakamakon hadarin, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.  (Saminu Alhassan)