logo

HAUSA

An gudanar da taron tattaunawa kan raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya tsakanin Sin da Girka

2023-10-30 20:47:32 CMG Hausa

Yau Litinin, babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya gudanar da taron tattaunawa kan raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya tsakanin Sin da Girka a birnin Athens na kasar Girka, inda tsohon shugaban Girka Prokopis Pavlopoulos, da shugaban kafar CMG Shen Haixiong, da ministar harkokin yawon shakatawa na Girka Olga Kefalogianni, da jakadan Sin dake Girka Xiao Junzheng, suka halarci taron.

Da yake jawabi, Shen Haixiong ya bayyana cewa, kasar Girka muhimmin bangare ne dake shiga aikin raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, kana ita ce muhimmiyyar abokiyar kasar Sin a nahiyar Turai. Ya ce ana raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ne domin musayar al’adu da koyi da juna tsakanin bangarori daban daban.

Shen Haixiong ya kara da cewa, bukukuwan al’adu da dama da aka bude a gun taron tattaunawar, su ne kashin bayan musayar al’adu tsakanin Sin da Girka, da samar da damar daidaita matsalolin duniya ta hanyar nazarin Sin da Girka masu daddadun al’adu.

A cewarsa, kafar CMG za ta yi hadin gwiwa mai zurfi a fannoni daban daban da kafofin watsa labarun Girka da bangarori daban daban na kasar don yin bayani da sa kaimi ga raya al’adun kasashen biyu. (Zainab)