Shirin Blue Circle Na Kasar Sin Ya Samu Lambar Yabo Ta Kare Muhalli Daga MDD
2023-10-30 20:28:06 CMG Hausa
Hukumar tsara shirin kiyaye muhalli na MDD wato UNEP, ya karrama shirin kare muhalli na Blue Circle na kasar Sin da lambar yabo mafi girma a fannin kare muhalli ta MDD ta shekarar 2023 wato “2023 Champions of the Earth Award”, saboda fasahar da ya kirkiro na sarrafa sharar teku.
A bana, shirye-shirye 5 daga 2,500 aka karrama. Daga cikinsu, akwai cibiyar binciken kimiyya da masana’antu ta kasar Afrika ta Kudu, wadda kokarinta ya bayar da gudunmuwa ga yaki da sharar roba a duniya, kamar yadda hukumar UNEP ta fada cikin sanarwarta.
Daga cikin rukunin shirye-shiryen da suka fito da sabbin dabaru, shirin Blue Circle ya yi amfani da fasahar adanawa da rarraba bayanai ta Blockchain da na’urorin masu fasahohin sadarwa wajen bibiyar baki dayan tsarin sharar roba, wanda ya hada da tattarawa da sarrafawa da sake samarwa da sayarwa.
Zuwa yanzu, shirin ya yi nasarar tattara ton 10,700 na burbushin cikin teku, wanda ya sanya shi zama shirin sarrafa sharar teku mafi girma a duniya. (Fa’iza Mustapha)