Isra'ila ta fadada kai hari ta kasa a Gaza
2023-10-30 10:53:24 CMG Hausa
Rahotanni na cewa, Isra'ila ta fadada harin da take kaiwa ta kasa a zirin Gaza, baya ga kara kai hare-hare ta sama a yankin da ta yi wa kawanya, yayin da adadin wadanda suka mutu a Gazan ya karu zuwa 8,005.
Kwanaki biyu bayan aika sojoji zuwa zirin Gaza, mai magana da yawun rundunar tsaron Isra'ila Daniel Hagari ya shaidawa manema labarai cewa, sojojin tsaronsu na kara dannawa zuwa zirin Gaza.
Ya ce, a halin yanzu hare-haren da sojojin ke kaiwa ta kasa, sun fi mayar da hankali ne kan arewacin zirin Gaza, kuma sannu a hankali suna fadada hare-hare ta kasa da kuma yadda sojoji suka danna a zirin Gaza.
Matakin na zuwa ne, a daidai lokacin da Isra'ila ta jibge dubban dakaru a kan iyakar Gaza, gabanin wani gagarumin farmaki da take shirin takaddamarwa ta kasa.
A jiya ne, ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, ya gana da wakilan iyalan mutane kusan 230 da Hamas ta yi garkuwa da su a harin da suka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. Yana mai cewa, harin da ake sa ran za a kaddamar ta kasa, na daga cikin kokarin dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su. (Ibrahim Yaya)