logo

HAUSA

Samar Da Hanyoyin Tabbatar Da Tsaro A Duniya Da Inganta Amincewa Da Juna A Taron Dandalin Tsaro Na Xiangshan

2023-10-30 16:27:56 CMG Hausa

Bisa la'akari da batutuwan tsaro da dama da duniya ke fuskanta, taron dandalin Xiangshan na birnin Beijing na kasar Sin karo na 10 ya kasance daya daga cikin muhimman tarukan tsara manufofin tsaro tare a duk duniya. A bana, mahalarta taron za su yi zama a nan birnin Beijing, domin tattauna batutuwan farko dake fuskantar tsaron kasashen duniya. 

Yaki da kalubalen tsaro da ke kunno kai daga wurare da lokutan da ba a yi hasashensu ba, na iya taimakawa wajen hada kan masu ruwa da tsaki a kan manufa daya, yayin da suke da ikon yin hadin gwiwa yadda ya kamata kan wadannan matsalolin da suke gurgunta ci gaban kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa. Duk da haka, wannan dandalin tsaro zai bankado cikakkun matakan tsaro don inganta zaman lafiya da bunkasuwa, da wadata ga dukkanin kasashe. Da tabbatar da duniyar zaman lafiya da kwanciyar hankali mai amfanar dukkan al'ummomi. 

Tun kafuwar dandalin a shekara ta 2006, dandalin tsaro na Xiangshan na Beijing, wanda ke kiyaye ka'idojin "Daidaito, Bude kofofi, Hadin kai, musayar ra’ayoyi", ya zama wani muhimmin dandalin tsaro na kasa da kasa. Dandalin yana daga cikin manyan tarukan tattaunawa kan manufofin tsaro na kasa da kasa a duniya, ta hanyar bude kafar tattaunawa don magance batutuwan da suka shafi tsaro na duniya, da habaka hadin gwiwa, da karfafa amincewar juna. Har ila yau, yana baiwa kasashe masu tasowa damar bayyana ra'ayoyinsu da kuma shiga harkokin tafiyar da harkokin tsaron duniya. Kasar Sin ta dauki nauyin dandalin ne domin inganta ra'ayoyinta kan muhimman batutuwan tsaro na kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da shirya tattaunawa da jami'an mahalarta taron. 

Taron dandalin na bana, mai taken "Tsaro na bai daya, zaman lafiya mai dorewa" ya mai da hankali kan shawarar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen duniya kan batun tsaro, yana baiwa dukkanin bangarori damar bayyana ra’ayoyinsu bisa daidato da adalci. Har ila yau, ana tattauna matsalolin tsaro, da bin hanyoyin samar da tsaro, da inganta hadin gwiwar tsaro. Za a gudanar da tarukan musamman guda takwas a lokaci guda da kuma zama hudu a dandalin na bana. Haka kuma, za a gudanar da turakan karawa juna sani a fannonin tsaro daban-daban musamman taron karawa juna sani na jami'an tsaro matasa da malamai masana harkokin tsaro. 

Taron na dandalin tattaunawa na Xiangshan na Beijin karo na 10 dake gudana daga ranar 29 zuwa ranar 31 ga watan Oktoba ya hada tawagogin hukuma daga kasashe sama da 90 da kungiyoyin kasa da kasa, gami da wakilai 22 a matakin ministan tsaro ko sama da haka, da wakilai 14 a matakin hafsan soji. Kana, fiye da masana 200 daga kasashe da yankuna sama da 50 sun nemi shiga dandalin. (Muhammed Yahaya)