Sherrie, mamallakin gidan abincin Thailand: Abinci gada ce da ke hada jama’ar Thailand da Sin
2023-10-30 20:37:07 CMG Hausa
Miyar Tom Yum Kung mai dadi, salak din gwanda mai wartsakarwa, da jatan-lanle da aka hadawa garin “curry” mai kamshi, ana iya dandana wadannan kayan abinci daga Thailand a gidan cin abinci na Sherrie. Ta yi aure daga birnin Bangkok na kasar Thailand zuwa birnin Beijing na kasar, Sherrie ta shigar da wata kadara mai ban mamaki a cikin abinci, wanda ke ba kowane mai cin abinci damar jin dadin da take ji. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani labari game da wannan baiwar Allah mai suna Sherrie, ‘yar kasar Thailand.
Lokacin da kuka bude kofar gilashi na wannan gidan cin abinci na Tailand, za a gaishe ku da kamshin “lemongrass” da ganyen mint. Yayin da kuke cikin gidan cin abincin Sherrie, kuna iya jin kamar kuna titunan Thailand.
“Mahaifiyata ta shafe shekaru sama da 20 tana gudanar da wani gidan abinci a Bangkok, girkinta yana da dadi sosai, irin abinci ne na arewacin Thailand, wanda ke da halin Thailand na gaske. Bayan na yi aure a nan birnin Beijing, sau da yawa ina tunanin dandanon abinci na garinmu, don haka, na tattauna da mijina, na kawo mahaifiyata, da ’yar’uwata, don bude wannan gidan cin abinci tare.”
Sherrie, wadda ta fito daga kasar Thailand, ta bude wani gidan cin abinci na Thailand a birnin Beijing shekaru biyu da suka wuce. Tun lokacin da ta bude wannan gidan cin abinci, ba wai kawai ya jawo hankalin masu cin abinci da yawa don dandana saboda ingantacciyar abinci ba ne, har ma ya samu tambarin takadar shaida ta "Zabin Thailand" daga Ma'aikatar Kasuwancin kasar.
Game da haka, Sherrie ta ce, wannan yana nufin cewa, gidan cin abinci nata shi ne mafi inganci wajen dafa abinci masu salon Tailand, ko ta fuskar dabarun dafa abinci, ko kayan abinci, da kuma kayan yaji.
“Akwai wani abokin ciniki na wanda yake matukar son miya mai tsami, kuma mai yaji da nake yi da kayan teku, kuma yana ci da yawa a duk lokacin da ya zo. Sai na ce masa, 'Bari in koya maka yadda ake yin shi?' Ya yi mamaki da kuma farin ciki, saboda ya dauka wannan miya ce sirrinmu, bai yi tsammanin zan koya masa ba. Akwai kuma wani abokin ciniki da ya tuko mota har zuwa nan daga wani wuri mai nisa, saboda matarsa tana son miyar Tom Yum Kung, don haka ya sayi miyar Tom Yum Gong mai nauyin kilo 10.”
Goyon baya da amincewar da ta samu daga wajen abokan ciniki, suna ta kara baiwa Sherrie karfin neman ci gaba. Bayan da ta yi zamanta a kasar Sin har tsawon shekaru da yawa, Sherrie ta kware sosai wajen dafa abinci na kasar Sin, irin su gogaggun kaji a cikin miya mai launin rawaya, da kifin kabeji da aka kawata... Har ma ta kware sosai wajen yin dafaffen dambu wato Jiao Zi. Ta ce, ana iya bayyana ainihin al'adun Thailand da Sin a cikin abincin.
“Abincin kasashenmu biyu ya dogara ne akan shinkafa a matsayin babban abinci, ina tsammanin irin wannan al’adar cin abincin tana wakiltar halin da muke ciki na yin hakuri, saboda shinkafa kadai ake iya ci tare da kowace tasa. Thailand kasa ce dake mayar da yawon bude ido a matsayin babbar hanyar samun kudin shiga, wannan ruhin maraba da kowa kamar yadda Sinawa suke darajanta zaman lafiya, da neman samun kudi ta hanyar zaman jituwa.”
'Ya'yan Sherrie guda biyu duk suna kasar Sin, daya yana makarantar firamare, dayan kuma yana gidan renon yara. A yayin mu'amalar yau da kullun da 'ya'yanta, Sherrie ta gano cewa, an shigar da kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin, da kyawawan dabi'un gargajiya na kasar cikin tsarin ba da ilmi a makarantun kasar ta Sin.
“Mutane daga kasashe daban-daban na iya rayuwa cikin jin dadi a kasar Sin. A halin yanzu, 'ya'ya na suna karatu makarantar Sinanci, suna wasa sosai da yara Sinawa yadda ya kamata a makaranta, suna taimakawa da koyi da juna, gaskiya ana jin kamar ‘Thailand da Sin iyali daya ne’. Malaman makarantar ma na kasancewa masu hakuri da yaran, kuma suna aiki tukuru wajen koya musu abubuwa da dama, da suka hada da al'adun kasar Sin da na kasa da kasa.”
Sherrie ta kara da cewa, wata rana 'yarta ta dawo daga makaranta ta ce da ita, “Ashe dai, kowane hatsin abinci a faranti an samo shi ne ta hanya mai wuyar gaske”, ma'anar jimlar ita ce, ya kamata mu dauki hatsi da martaba ba tare da barnatawa ba. Don haka, a ganin ta, malaman kasar Sin suna da kwarewa sosai, tana kuma gode musu sosai.
Sherrie ta ce, yayin da mu'amalar cinikayya da al'adu tsakanin Thailand da Sin ke karuwa a cikin 'yan shekarun nan, Sinawa da yawa suna cike da sha'awar al'adun abinci na Thailand.
“A cikin 'yan shekarun nan, an samu karuwar gidajen cin abinci na kasar Thailand a nan birnin Beijing, ciki har da gidajen cin abinci dake da rassa, da wadanda suke dafa abinci a gida kamar ni, da wasu masu dafa abinci na fada, da kuma wasu rumfunan sayar da abinci dake samun karbuwa saboda marbata abotar su. Baya ga haka, na kan ga wasu gajerun bidiyo da yawa da aka dauka game da koya wa mutane yadda ake dafa abincin Thailand a yanar gizo, wasu hanyoyin da suke bi suna da salon Thailand sosai, bayan na gansu, na kan ba su babban yatsa a kasa da bidiyoyin.”
Sherrie ta ce, yanzu dai, mutanen Thailand suna sha'awar wasu abincin kasar Sin sosai, ciki har da tukunyar yaji, gasa abinci wato barbecue, da alewar tsinke, wadanda ake iya samun su a cikin kowace kasuwa da dare. Tana ganin wadannan ba za su iya rabuwa da mu'amalar kut da kut da ake yi a tsakanin kasashenmu biyu ba.
Har ila yau, Sherrie tana fatan gina "gadar abinci masu dadi" don sada zumunci tsakanin Thailand da Sin, tare da kai abokantakar dake tsakanin kasashen biyu da suka dade suna sadawa wani sabon matsayi.
“A cikin salak din koriyar gwanda na Thailand, za mu iya kara wasu abubuwa da yawa, kamar kwan agwagwa mai gishiri. Bayan na zo kasar Sin, na yi matukar farin ciki da ganin Sinawa su ma suna son cin kwan agwagwa mai gishiri. Abinci wata gada ce da ke hada mutanen kasashen biyu. Muna da wata magana a Thailand, wato "myna and baffalo", ina son wannan karin magana sosai, tana wakiltar amincewa juna, da taimakon juna da cin moriyar juna. Kasashen Thailand da Sin suna amincewa da juna, kuma abokai ne na kwarai da ke taimakon juna, kuma nan gaba za su ci gaba da neman bunkasuwa tare.”