Hun Manet: Kasar Kambodiya Na Goyon Bayan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”
2023-10-30 15:23:18 CMG Hausa
Kwanan nan, firaministan Kambodiya Hun Manet, ya halarci taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “Ziri Daya da hanya daya” karo na uku a birnin Beijing. A lokacin da ya yi hira da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, Hun Manet ya bayyana cewa, bangaren Kambodiya ya halarci taron sau uku a jere, wanda ya shaida yadda take goyon bayan kokarin bunkasa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, tare da kuma taron kansa.
Ya ce wannan ne karo na farko da ya halarci taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ya kuma taya shugaban Sin Xi Jinping da gwamnatin Sin murnar gudanar da taron cikin nasara. Ya kara da cewa, mahalarta sun zo daga sassan duniya daban daban, musamman ma kasashe masu tasowa, kuma Kambodiya ta hada manufofin ci gaba tare da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, wanda ya kawo babban alheri ga kasarsa. (Safiyah Ma)