logo

HAUSA

Isra'ila ta sanar da mayar da wani bangare na samar da ruwan sha a zirin Gaza

2023-10-30 10:38:15 CMG Hausa

Jiya Lahadi 29 ga watan nan ne Isra'ila ta sanar da mayar da wani bangare na aikin samar da ruwan sha a zirin Gaza, wanda zai rika samar da ruwa har lita miliyan 28 a ko wace rana.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayar da rahoton cewa, ofishin kula da harkokin yankunan gwamnatin kasar da ke karkashin ma'aikatar tsaron kasar, ya bayyana a wannan rana cewa, Isra’ila ta riga ta sake bude bututun ruwa guda biyu da ke zuwa zirin Gaza, inda ko wace rana suke kai ruwa har lita miliyan 28 zuwa Gaza. An ce kafin barkewar rikicin na wannan karo, Isra'ila na sayar da ruwa har lita miliyan 49 ga zirin Gaza ta bututu guda uku a ko wace rana.

A baya-bayan nan, hukumar ba da agaji da ayyuka ta MDD ta sanar da cewa, tun bayan barkewar sabon rikici tsakanin Falasdinu da Isra'ila, cibiyoyin tace ruwan sha guda uku dake zirin Gaza sun daina aiki saboda karancin mai.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)