logo

HAUSA

Gwamantin jihar Jigawa ta rabar da motocin noma 54 ga kananan hukumomin jihar

2023-10-30 12:28:14 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Jigawa dake arewacin Najeriya ta ce, ta shirya tsaf domin noma hekta dubu 40 na gonar alkama a yayin noman rani na bana.

Gwamnan jihar Umar Namadi ne ya tabbatar da hakan a Dutse yayin bikin kaddamar da rabon motocin noma guda bi-biyu ga kananan hukumomin jihar 27.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Motocin noma da aka raba dai suna hade ne da dukkannin kayayyakin noma da suka hadar da garmunan huda da na’urorin casa.

Gwamna Umar Namadi ya ce, za a gudanar da noman alkama ne bisa hadin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma bankin raya kasashen Afrika.

Ya ci gaba da cewa:

“A wannan rana muna mika motocin noma guda 54 inda kowanne shugaban karamar hukumar daga cikin kananan hukumomin jihar 27 ya sami mota biyu, mun yi hakan ne ganin cewa shugaban karamar hukuma shi ya fi kusa da jama’a, shi ne kuma ya fi sanin jama’a, duk wani korafi da mutumin karkara yake da shi wajen shugaban karamar hukumar yake fara zuwa, shi ne muka ga dacewa damka masu motoci domin tabbatar da ganin manoman karkara sun ci gajiyarsu.” (Garba Abdullahi Bagwai)