logo

HAUSA

Wang Yi: Har Yanzu Dangantakar Sin Da Amurka Na Da Kuzari

2023-10-29 16:54:34 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan kungiyar ‘yan kasuwa ta kasar Amurka, za ta kyautata ra’ayin jama’a da karfafa tubalin abotar Sin da Amurka, da kuma bayar da sabbin gudunmuwa ga ingantawa da raya dangantakar kasashen biyu.

Wang Yi ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilan kungiyar ‘yan kasuwa ta Amurka, jiya Asabar a birnin Washington. Inda ya ce, har yanzu dangantakar kasashen biyu na da karfi.

Mahalarta tattaunawar sun ce, muradun Sin da Amurka na hade da juna, kuma dangantaka mai karfi a tsakaninsu, na da muhimmanci ga nasararsu baki daya. Haka kuma, kungiyar tana bayar da muhimmanci ga ci gaban Sin mai inganci, kana tana da kwarin gwiwa kan kasuwar kasar Sin da goyon bayan kasashen biyu wajen daukar matakan da suka dace na saukaka musaya tsakanin jama’arsu. (Fa’iza Mustapha)