logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Tattauna Da Masana Tsara Manufofi Na Amurka

2023-10-29 16:21:00 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ke ziyara a kasar Amurka, ya tattauna da masana tsara manufofi na Amurka, jiya Asabar a birnin Washington.

Wang Yi ya ce, yayin ziyararsa, bisa yanayi na daidaito da girmmama juna, Amurka da Sin sun yi tattaunawa mai zurfi kuma mai ma’ana kan batutuwan dake jan hankalinsu, haka kuma sun aike da kyakyyawan sako game da daidaitawa da inganta dangantakarsu.

Ya kara da cewa, duk da sabani da takkadamar dake akwai tsakanin kasashen biyu, da tarin batutuwan da ba a shawo kansu ba, bangarorin biyu sun yi imanin cewa, ya zama wajibi kuma abu ne mai amfani su ci gaba da tattaunawa a matsayinsu na manyan kasashe.

A nasu bangare, mahalarta tattaunawar sun bayyana cewa, kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka ta dace da muradun kasashen biyu. Haka kuma, za ta taka muhimmiyar rawa wajen warware muhimman batutuwan yankuna da na duniya baki daya.

Sun kara da cewa, yayin da ake fuskantar rikice-rikice a yankuna da rashin oda a duniya, ya zama wajibi Amurka da Sin su karfafa tuntubar juna da hada hannu wajen shawo kan kalubale. (Fa’iza Mustapha)