logo

HAUSA

An mayar da hidimar sadarwa a zirin Gaza

2023-10-29 16:54:37 CMG Hausa

Kamfanin sadarwa na Palesdinu ya sanar da sanyin safiyar yau cewa, an mayar da hidimar sadarwa da ta hada da ta wayar tarho da wayar salula da kuma yanar gizo a zirin Gaza sannu a hankali.

Firaministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a daren jiya a birnin Tel Aviv-Yafo cewa, shigar karin sojojin kasa na Isra’ila cikin zirin Gaza, ya shaida shiga mataki na biyu na yaki da kungiyar Hamas. Kuma burin sojojin Isra’ila shi ne, murkushe karfi da ikon kungiyar Hamas na aiwatar da ayyukanta, tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su don mayar da su gida.

A nata bangare, ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar a jiya cewa, harin kasa da sojojin Isra’ila suka kaiwa zirin Gaza zai kawo hadari da babbar illa ga yanayin jin kai da tsaro a yankin, kuma karin ayyukan soja da Isra’ila za ta gudanar za su haddasa karuwar asarar rayuka ko raunatar fararen hula da dama, ciki har da kananan yara da mata. Har ila yau, Masar ta bukaci gwamnatin Isra’ila da ta dauki alhakin sabawa kudurin babban taron MDD, tana mai yin kira ga Isra’ila da ta samar da cikakkiyar gudummawar jin kai mai dorewa da aminci ga zirin Gaza.

Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta zirin Gaza na Palesdinu ta gabatar a jiya, mutane 7,703 sun mutu, kana wasu 19,743 sun jikkata sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai zirin Gaza. (Zainab)