logo

HAUSA

Jihar Sokoto tare da wata kungiyar lafiya sun kaddamar da aikin riga-kafi ga kananan yara

2023-10-28 16:30:05 CMG Hausa

Kimanin kananan yara dubu 20 ne ake sa ran za su amfana daga wani shirin hadin gwiwar allurar riga-kafin wasu nau`ikan cututtuka dake saurin halaka kananan yara `yan kasa da shekaru biyar da haihuwa a jihar Sokoto ta arewacin Najeriya.

Kungiyar kiwon lafiyar yara ta Sight-savers ce ta ke gudanar da shirin bisa tallafin gwamnatin jihar ta Sokoto, inda aka fara gwaji daga yankin karamar hukumar Wamako kafin kaiwa ga sauran kananan hukumomi.

Daga tarayyyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi bagwai ya aiko mana da rahoto.

Rahotannin da hukumomin duniya kamar Unicef da hukumar Lafiya ta duniya WHO suka fitar sun nuna cewa jihar Sokoto na daga cikin jahohin Najeriya da ake fama da mace-macen kananan yara, inda suka ce a shekara ta 2023 kadai cikin yara dubu 100 da ake haifa, yara dubu daya da dari biyar da saba`in da shida ne suke mutuwa ta dalilin cututtuka daban daban, ko da yake rahoton ya nuna cewa adadin ya ragu mutuka idan aka kwatanta da shekarar bara ta 2022.

Malam Bashir Garba shi ne babban jami`in allurar riga-kafi na hukumar lafiya matakin farko na jihar Sokoto ya yi karin bayani a game da jerin cututtuka da za a yi riga kafin akan su, kuma kamar yadda yace ana auna nauyin kowanne yaro a yayin aikin tantance matsayin koshin lafiyar sa.

“Wannan magani yana da mutukar muhimmanci kuma ya zo lokacin da ya kamata, duba da irin yara `yan kasa da shekaru biyar da suke rasa rayukan su, kusan kashi 20 cikin dari kowacce shekara su kan mutu sanadiyar wadannan cututtuka, irin su ciwon hakarkari, tarin fuka da gudawa da kuma abun da ake cewa maci dan wawa wato cutar barewar fatar jiki wadda ke nuna alamu kamar na kuna, saboda haka an zabi karamar hukumar Wamako domin a yi gwaji, idan Allah ya sa an kammala, nasarorin da aka samu, shi zai sa a kaddamar da shirin zuwa ga sauran kananan hukumomi 23”

A yanzu haka dai irin wannan shiri na cigaba da gudana a jahohin Kano da Akwa-Ibom da Kebbi da kuma jihar Jigawa.(Garba Abdullahi Bagwai)