logo

HAUSA

Wakilin Sin: Kudurin babban taron MDD ya nuna ra’ayin kasashen duniya na tsagaita bude wuta da kawo karshen yaki a tsakanin Falasdinu da Isra'ila

2023-10-28 16:57:34 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya ce, kasarsa ta yi maraba da zartar da kuduri game da yanayin da ake ciki tsakanin Falasdinu da Isra’ila a babban taron MDD, wanda ya nuna gagarumin kira daga akasarin kasashe mambobin kungiyar na tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin.

Jami’in ya bayyana hakan ne bayan da aka zartas da kudurin a taron gaggawa na MDD da aka shirya a jiya Jumma’a ranar 27 ga wata, inda ya kara da cewa, kasar Sin na fatan za a tabbatar da wannan kuduri a dukkan fannoni. Kana Sin tana matukar yabawa kuma za ta ci gaba da ba da goyon baya ga kasashen Larabawa da na Musulunci wajen taka muhimmiyar rawa kan batun Falasdinu.

Babban taron gaggawa na MDD ya zartar da wani kuduri kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra'ila, wanda Jordan ta gabatar a madadin kasashen Larabawa, sakamakon kuri'un da aka samu na amincewa 120, na adawa 14, yayin da aka samu na janye jiki 45.

Kudurin ya yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta na jin kai cikin dogon lokaci, ta yadda za a dakatar da ayyukan nuna gaba da juna. Kudurin dai ya bukaci dukkan bangarori masu ruwa da tsaki su mutunta dokokin kasa da kasa, da kuma kare fararen hula.

Kudurin ya sake tabbatar da cewa, ya kamata a nemi hanyar adalci da dorewa kan rikicin Falasdinu da Isra'ila bisa “shirin samar da kasashe biyu".

Kasar Sin ta kasance mai daukar nauyin wannan kuduri tare da kada kuri'ar amincewa a yayin kada kuri'ar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)