logo

HAUSA

Isra’ila ta tsananta kai hare-hare a Gaza bayan da sojoji suka fadada ayyukansu

2023-10-28 17:35:52 CMG

An ga tashin bama-bamai da dama a Gaza a ranar 28 ga watan Oktoba bayan da sojojin Isra’ila suka ce dakarunsu na kasa za su fadada ayyukansu a yankin Falasdinawa da suka yiwa kawanya.

Sanarwar ta zo ne sa'o'i bayan ministan tsaron Isra'ila ya ce kasar na sa ran kaddamar da hare-hare ta kasa na dogon lokaci a zirin Gaza. Jim kadan kafin sanarwar, aka katse ayyukan sadarwa a yankin. (Yahaya)