logo

HAUSA

Kasashen Larabawa 9 sun bukaci kwamitin tsaron MDD da ya tursasawa sassan dake yaki a Gaza su amince da tsagaita wuta

2023-10-27 10:51:45 CMG Hausa

Kasashen Larabawa 9, sun bukaci kwamitin tsaron MDD da ya tursasawa sassan dake gwabza fada a zirin Gaza, da su amince da tsagaita bude wuta nan take.

Ministocin wajen kasashen Masar, da Jordan, da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain, da Saudiyya, da Oman, da Qatar, da Kuwait, da Morocco, sun gabatar da takardar hadin gwiwa ga ‘yan jaridu a jiya Alhamis, wadda ke bayyana takaicin kasashensu, game da yadda ake kaiwa fararen hula farmaki, suna masu kira da a dakatar da dukkanin wani dauki ba dadi, da keta dokokin kasa da kasa, ciki har da na jin kai, da na kare hakkokin bil Adama.

Bugu da kari, kasashen 9 sun yi Allah wadai, tare da watsi da duk wani yunkuri na daidaikun mutane, ko gamayyar wasu sassa, na hukunta wasu al’ummu ba tare da la’akari da wadanda ba su ji ba ba su gani ba. (Saminu Alhassan)