logo

HAUSA

Wang Yi ya yi shawarwari tare da sakataren harkokin wajen kasar Amurka

2023-10-27 14:42:44 CMG HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da takwaransa na Amurka Antony Blinken a ranar 26 ga wata bisa agogon wurin a yayin ziyarar gayyata da yake yi a kasar.

Inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, da wasu abubuwan da ke jawo hankalinsu tare. Ana sa ran cewa, za su ci gaba da tattaunawa da safiyar ranar 27 ga wata bisa agogon wurin. (Amina Xu)