logo

HAUSA

Shin wasan kwaikwayon na zaben kakakin majalisar wakilan Amurka ta kawo karshe ne?

2023-10-27 14:21:20 CMG Hausa

An kawo karshen kiki-kakar siyasar Amurka da ya shafe tsawon makonni 3 a jiya, inda dan majalisa daga jam’iyyar Republican, Mike Johnson ya samu kuri’u 220 da suka kai shi ga zama sabon kakakin majalisar wakilan kasar. Sai dai, sakamakon ya zo a wani yanayi na wasan kwaikwayo, saboda yadda rikicin cikin gida a tsakanin ’yan jam’iyyar Republican, inda aka yi ta watsi da ’yan takara 3 na baya, daya bayan daya. Haka kuma, zaben ya fuskanci tarin matsaloli. Ko hazikan marubuta labaran zube, ba za su yi irin haka ba.

Bisa yadda aka fasalta, tsarin demokradiyyar Amurka ba shi da tawaya. ’Yan siyasa na taka tsantsa da kai zuciya nesa da fahimtar daidaiton da ya kamata a fannonin bukatun kai da na jam’iyya da muradun kasa. Sai dai, a zahiri, galibin ’yan majalisar dake da matukar son kai, ba sa la’akari da muradun jam’iyya ko kasar. Don haka, akwai rashin da cewa tsakanin wannan tsarin demokradiyya da zahirin yanayin siyasar Amurka, wanda ke haifar da rikicin cikin gida a jam’iyya da fito na fito da juna.

A wannan wasan kwaikwayo na zaben kakakin majalisar wakilan Amjurka, an ga tsananin son kai a zahiri. Amma tsarin siyasar kasar bai dauki matakan magance wannan matsala ba. Wanna ba matsala ba ce da wani zai iya magancewa ba. (Fa’iza Mustapha)