CMG ya gudanar da bikin kaddamar da shirin “Journey Through Civilizations” a kasar Masar
2023-10-27 20:56:07 CMG Hausa
Jiya Alhamis 26 ga wata ne, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gudanar da wani biki don kaddamar da nune-nunen “Journey Through Civilizations” wato hanyar fahimtar wayewar kai a cibiyar al’adun kasar Sin dake Alkahira, babban birnin kasar Masar. Mataimakin shugaban sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban CMG, Shen Haixiong ya yi jawabi ta kafar bidiyo.
A yayin jawabinsa, Shen Haixiong ya bayyana cewa, a cikin dogon tarihi, kyawawan wayewar kan kasar Sin da na tsohuwar kasar Masar sun ba da gudummawa sosai ga ci gaban wayewar kan dan Adam. Bisa ga kyakkyawan tsarin shawarar wayewar kai ta duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, jama'ar kasar Sin suna aiki tukuru don gina al'ummar kasar mai wayewar kai ta zamani, da sa kaimi ga neman sabon ci gaban wayewar kan dan Adam. Shen Haixiong ya kara da cewa, CMG zai tabbatar da aikin watsa labaru, da yin kirkire-kirkire, da yada wayewar kan kasar Sin, da karfafa mu'amalar al'adu tsakanin Sin da kasashen Larabawa, da sa kaimi ga yin shawarwari tsakanin al'ummomin Sin da kasashen Larabawa, da ba da hikimomi da karfi wajen bunkasa fahimtar juna da dankon zumunci tsakanin jama'ar Sin da kasashen Larabawa, da inganta gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da kasashen Larabawa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)